'Yan Adawa A Kenya Sun Yi Maraba Da Soke Zabe
'Yan adawa a kasar Kenya ta yi maraba da matakin kotun kolin kasar na soke zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan jiya.
Jagoran 'yan adawa na kasar Raila Odinga ya ce, wannan shi ne irinsa na farko a nahiyar Afrika, don haka abun yabawa ne.
A cikin wata sanarwa ce da ta fitar a yau kotun Kolin Kenya ta soke zaben shugabancin kasar da aka gudanar a ranar 8 ga watan Agusta da ya gabata, inda aka ayyana Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya yi nasara, To sai dai kotun kolin ta ce sakamakon da aka fitar cike yake da magudi.
Kotun ta bada umarnin sake gudanar da babban zaben kasar nan da kwanaki 60 masu zuwa, bayan da babban alkalin ta David Maraga ya bayyana soke zaben.
Sai dai shugaba Uhuru Kenyatta ya ki amince wa da hukucin kotun, amma duk da haka zai mutunta umarninta kamar yadda ya shaida wa manema labarai.