Najeriya : Kwalera Ta Kashe Mutum 14 A Sansanin 'Yan gudun Hijira
Hukumomin kiwon lafiya a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya sun sanar da mutuwar mutane 14 sanadin kamuwa da cutar amai da gudawa a wani sansanin 'yan gudun hijiran Boko Haram.
Wata sanarwa da ma'aikatar kiwon lafiya yankin ta fitar ta ce a ranar 1 ga watan Satumban nan ta samu rahoton mutuwar mutanen 14, a yayin da adaddin wadanda ake kyautata zaton sun kamu da cutar ya kai 186.
Mafi yawan wadanda lamarin ya shafa mazauna yankin Muna Garage ne wanda wani sansanin 'yan gudun hijira ne dake kewayen birnin Maiduguri babban birnin jihar Borno wanda ya sha fama da matsalar Boko Haram.
Sanarwar ta ce tuni aka dauki matakai da suka danganci saftace ruwan sha, da karin wuraren tsugunni, a yayin da ma'aikatan lafiya da kungiyoyi masu zaman kansu na yankin suka fara waye kanuwan jama'a akan matakan dauka na hana yaduwar cutar.
Alkalumma sun nuna cewa mutane sama da 20,000 ne suka rasa rayukansu sanadin rikicin Boko Haram, a yayin da wasu miliyan biyu da dari shida suka kauracewa muhallansu wanda galibinsu ke tsugunne a sansanonin 'yan gudun hijira, dake fuskantar barazana karancin abinci da kuma cututtuka irin su zazzabin malariya.