Rikici Ya Sake Kunno Kai Tsakanin Sudan Da Masar Kan Yankin "Hala'ib"
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23725-rikici_ya_sake_kunno_kai_tsakanin_sudan_da_masar_kan_yankin_hala'ib
Rahotanni daga kasar Sudan suna nuni da cewa wani sabon rikici ya sake kunno kai tsakanin kasar da kasar Masar dangane yankin "Hala'ib" da Sudan din take ganin yankin kasar ne da Masar ta mamaye.
(last modified 2018-08-22T07:00:38+00:00 )
Sep 03, 2017 06:20 UTC
  • Rikici Ya Sake Kunno Kai Tsakanin Sudan Da Masar Kan Yankin

Rahotanni daga kasar Sudan suna nuni da cewa wani sabon rikici ya sake kunno kai tsakanin kasar da kasar Masar dangane yankin "Hala'ib" da Sudan din take ganin yankin kasar ne da Masar ta mamaye.

Rahotanni sun jiyo gwamnan jihar "Al Bahr al Ahmar" (Red Sea) na kasar Sudan din Ali Ahmad Hamid yana fadin cewa yankin "Hala'ib" din yanki ne na kasar Sudan duk kuwa da mamaye yankin da kasar Masar take ci gaba da yi, yana mai cewa ko shakka babu yankin zai ci gaba da zama mallakar kasar Sudan.

Kafin hakan ma dai ministan harkokin wajen kasar Sudan din Ibrahim Ghandour ya bayyana cewar rikicin da ke tsakanin Sudan da Masar yana nan daram kuma zai ci gaba da zama karfen kafa cikin kyautatuwar alaka tsakanin kasashen biyu,

Tun daga lokacin samun 'yancin kasar Sudan a shekarar 1956, ake rikici tsakanin kasashen Masar da Sudan kan yankin na "Hala'ib", sannann kuma sojojin Masar sun mamaye yankin ne bayan kokarin da wasu suka yi na kashe tsohon shugaban Masar din Hosni Mubarak a taron shugabannin kasashen Afirka a birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia.