An Kashe Mutane Sama Da 30 A kasar Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23728-an_kashe_mutane_sama_da_30_a_kasar_somaliya
Kimanin sojoji 26 ne suka hallaka yayin da wasu fararen hula 12 suka rasa rayukansu sanadiyar wani mumunar hari na mayakan kungiyar As-shabab
(last modified 2018-08-22T11:30:38+00:00 )
Sep 03, 2017 18:54 UTC
  • An Kashe Mutane Sama Da 30 A kasar Somaliya

Kimanin sojoji 26 ne suka hallaka yayin da wasu fararen hula 12 suka rasa rayukansu sanadiyar wani mumunar hari na mayakan kungiyar As-shabab

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto wata majiya a somaliya na cewa, mayakan kungiyar As-shabab sun kai wani mumunar hari a sansanin sojin kasar dake tsibirin Kismaayo tare da hallaka jami'an tsaro 26.

Har ila yau kungiyar ta Ashabab ta kai wani hari na ta'addanci a wani kauye dake kudancin garin Bousasou na arewacin kasar tare da kashe akalla mutane 12, biyar daga cikin su sojojin kasar ne.

kafin hakan dai, a watan yulin da ya gabata,mayakan na As-shabab sun kai irin hari a garin Bousasou tare da hallaka fararen 38.

Shekaru da dama kungiyar ta As-shabab ta kwashe tana yaki da gwamnatin kasar Somaliya, a wata augustan 2011, dakarun tsaron kasar somaliyan tare da hadin gwiwar dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashen Afirka sun kaddamar da wani gagarimin hari kan mayakan na Ashabb tare da kwace birnin magadushu fadar milkin kasar daga hanunsu.