Gwamnatin Gabon Ta Hana Madugun 'Yan Adawan Kasar Jean Pean Barin Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23743-gwamnatin_gabon_ta_hana_madugun_'yan_adawan_kasar_jean_pean_barin_kasar
Gwamnatin kasar Gabon ta haramta wa madugun 'yan adawan kasar Jean Ping da wasu na kurkusa da shi fita daga kasar bayan kiran da suka yi a gudanar da wani gagarumin yunkuri na gama gari da nufin kawar da shugaban kasar Ali Bongo Ondimba daga karagar mulki.
(last modified 2019-01-16T04:00:45+00:00 )
Sep 04, 2017 06:18 UTC
  • Gwamnatin Gabon Ta Hana Madugun 'Yan Adawan Kasar Jean Pean Barin Kasar

Gwamnatin kasar Gabon ta haramta wa madugun 'yan adawan kasar Jean Ping da wasu na kurkusa da shi fita daga kasar bayan kiran da suka yi a gudanar da wani gagarumin yunkuri na gama gari da nufin kawar da shugaban kasar Ali Bongo Ondimba daga karagar mulki.

Ministan cikin gidan kasar Gabon din Noel Matha ne ya sanar da hakan inda ya ce an sanya wa Jean Pean din da mukarrabansa wannan takunkumin ne a matsayin mayar da martani ga sanarwar da Mr. Jean Pean din ya fitar inda ya kirayi mutane zuwa ga bore da kuma yakin basasa in ji ministan.

Yayin da suke mayar da martani ga wannan sanarwar, jam'iyyar Mr. Jean Pean din ta ce hakan karen tsaye ne ga hakkokin su wanda kuma ba su yi mamakin hakan ba daga wajen gwamnatin.

Mr. Pean dai ya sanar da kansa a matsayin zababben shugaban kasar bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar inda aka sanar da shugaba Bongon a matsayin wanda ya lashe zaben, yana mai zargin shugaba Bongon da amfani da rashawa da kuma karfi wajen ci gaba da zama kan kujerar mulki.