Kenya : Hukumar Zabe Ta Tsaida Ranar Sake Zaben Shugaban Kasa
(last modified Mon, 04 Sep 2017 19:10:21 GMT )
Sep 04, 2017 19:10 UTC
  • Kenya : Hukumar Zabe Ta Tsaida Ranar Sake Zaben Shugaban Kasa

Hukumar Zabe a kasar Kenya ta bayyana ranar 17 ga wata Oktoba mai zuwa a matsayin ranar da za'a sake zaben shugaban kasa tsakanin shugaban mai ci Uhuru Kenyata da kuma Raila Odingi shugaban babbar jam'iyyar yan adawar kasar.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa yan takara biyu ne kadai zasu shiga zaben, wato shugaba mai ci da kuma shugaban babban jam'iyyar adawar kasar,

Image Caption

 

.

A ranar 8 ga watan Augusta ne aka gudanar da zaben shugaban kasa a cikin yan takara 4, inda sakamakon zaben ya nuna cewa Uhuru Kenyata ne ya lashe zaben da tazararv kuri'u miliyon 1.4 tsakaninsa da mai binsa wato Raila Odinga. 

Kakakin fadar shugaban kasa dai ya ce gwamnati ba zata sauya ko da guda daga cikin ma'aikatan hukumar zaben ba, a yayinsa shi kuma shugaban yan adawa ya bukaci babban kotun kasar ta sallami wasu daga cikin shuwagababannin hukumar zaben ta kuma gurfanar da su a gaban kuliya.

Alkalin Alkalai na kasar chief justice David Maraga ya yanke hukuncin bata sakamakon zaben a ranar 1 ga watan Satumba da muke ciki amma ya ki korar ma'aikatan zaben, don a fadinsa ba zai iya yin haka ba sai ya duba takardun korafe-korafe kimani 80,000 da aka mika masa. Don haka ya ce nan da ranar 21 ga watan da muke ciki zai yanke hukunci a kan lamarin.