Bukatar Gwamnatin Jamhuriyar D/Congo Ga 'Yan Adawa
A yayin da rikicin siyasa ke kara kamari a kasar D/congo, ministan tattalin arzikin kasar ya bukaci 'yan adawa da su hau kan tebirin tattaunawa tare da gwamnati.
Ministan tattalin arzikin kasar D/congo Joseph Kapika ya kira 'yan adawa da su hau kan tebirin tattaunawa tare da gwamnatin kasar, inda ya ce matsalar da ake fuskanta a yanzu ana iya magance ta ta hanyar tattaunawa, sannan ya bukaci 'yan adawa da su kawo karshen zanga-zangar da suke yi, domin wasu na amfani da wannan zanga-zanga wajen tayar da tarzoma gami da tashin hankali a kasar.
Wannan bayyani na ministan tattalin arzikin kasar ta Congo na zuwa ne a yayin da taron magoya bayan madugun 'yan adawar kasar Felix Tshisekedi ya rikida zuwa ga rikici da tashin hankali, kafin hakan dai, 'yan adawar nada niyar gudanar da wani gagarimin gangami a ranar 4 ga watan Satumba, saidai gwamnati ta hana wannan gangami bisa dalilai na tsaro.
Kasar D/Congo ta fada cikin rikicin siyasa ne tun bayan da gwamnati ta dage zaben shugaban kasar da kuma dagewa shugaba kabila na ci gaba da zama a kan karagar milki, duk da cewa a cikin wannan yanayi na rikici, bangaren 'yan adawa da 'yan majalisar dokokin kasar sun cimma matsaya na gudanar da zaben shugaban kasa, to amma a yanzu 'yan adawa na zargin gwamnatin joseph kabila da karya wannan yarjejeniya.
A kwanakin baya,Jean-Pierre Lacroix wakilin sakatare janar na MDD a kan al'amuran sulhu ya fada a kwamitin tsaron MDD cewa a yayin da rage lokaci kadan a gudanar da zaben shugaban kasa a jamhuriyar D/Congo, har yanzu babu wani shiri da 'yan siyasa ke yi na shirye-shiryen gudanar da zabe a kasar.
A nasu bangare 'yan adawa na jirar zartar da yarjejjeniyar da aka cimma daga bangaren gwamnati, inda ake sa ran Shugaba Kabila zai sauka daga kan karagar mulki, sai dai a nata bangare, hukumar zaben kasar ta bayyana cewa akwai yiyuwar sake daga zaben shugaban kasar.
Christopher Luthendula daya daga cikin shugabanin jam'iyun adawar kasar kuma mataimakin shugaban gamayyar jam'iyun 'yan adawa 7 na kasar ya bayyana cewa sake dage zaben ya saba wa kundin tsarin mulki da kuma yarjejeniyar da aka cimma a ranar 31 ga watan Disamba na 2016, kuma wannan kudiri na nuna da cewa matukar dai Shugaba Joseph Kabila na kan karagar mulki, ba za a gudanar da zaben Shugaban kasar ba.
Kokari na ci gaba da zama a kan karagar mulki ta hanyar canza kundin tsarin mulki gami da murguda zabe ya zamanto babbar matsalar da da dama daga cikin kasashen Afirka ke fuskanta, 'yan adawar Joseph Kabila na nuna damuwarsu game da yanayin siyasa da kasar ke ciki,domin ci gaba da zaman Kabila a kan karagar mulki ya sabawa kundin tsarin mulki da kuma tsarin tafarkin Demokaradiya na kasar, rashin 'yancin siyasa, hana gudanar da taron siyasa tare amfani da karfi wajen tarwatsa 'yan adawa na daga cikin ababen da 'yan adawa ke nuna damuwa a kan su a kasar ta Congo.
A halin da ake ciki, kasar ta Congo ta shiga cikin wani sabon rikicin siyasa, wanda masu sharhi ke ganin cewa ana iya magance shi, idan aka yi amfani da da yarjejeinyar da aka cimma ta 2016,idan kuma ba hakan ba, ba za a fitar da tsamanin yakin ciki gida ba a kasar ta D/Conogo.