An Kashe Babban Hafsan Sojin Kasar Lesotho
Rahotanni daga Lesotho na cewa an kashe babban hafsan sojin kasar, Janar Khoantle Motsomotso, a yayin wata musayar wuta a barikin soji.
Ko baya ga babban hafsan sojin kasar, da akwai wasu mayan sojoji biyu da suka hada da Kanal Tefo Hashatsi da Janar Bulane Sechele da suka gamu da ajalinsu a cikin lamarin na yau Talata
Bayanai sun ce wasu sojoji biyu ne suka nemi kusawa da karfi a cikin ofishin babban hafsan sojin kasar a yayin da gumurzu ya barke tsakaninsu da masu gadin Janar din.
Wannan lamari dai na zuwa ne watanni uku bayan zaben da ya kawo firaministan kasar Thomas Tabane a madafun iko.
Dan shekaru 78, Mista Tabane ya kama mulki a kasarsa a watan Yuni bayan shekaru uku na gudun hijira a kasar Afirka ta Kudu sanadin yunkurin mulkin soji.