Gabon : An Kori Ministan Muhalli
Sep 08, 2017 04:41 UTC
Gwamnatin Gabon ta sallami ministan muhalli da mayan gine gine na kasar, Bruno Ben Moubamba daga bakin aikinsa.
An dai sanar da korar ministan ne bisa umurnin firayi ministan kasar saboda aikata babban laifi, kamar yadda aka sanar a gidan talabijin din kasar.
Ana dai zargin Ministan ne da sukar magabatansa, a cewar firayi ministan kasar.
Shi dai ministan ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na facebook wasu kalamai da ke zargin firayi ministan kasar da kawo cikas ga wani shirinsa na yin tsari ga harkokin mallakar filaye a fadin kasar domin yin gidaje ta yadda talakawa zasu mallaki gidaje ko filayen kansu.
Tags