Ivory Coast : An Zargi Makusantan Gbagbo Da Neman Tada Fitina
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23833-ivory_coast_an_zargi_makusantan_gbagbo_da_neman_tada_fitina
Gwamnatin Ivory Coast, ta zargi makusantan tsohon shugaban kasar, Laurent Gbagbo, da kokarin tana zaune tsaye a kasar.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Sep 08, 2017 05:01 UTC
  • Ivory Coast : An Zargi Makusantan Gbagbo Da Neman Tada Fitina

Gwamnatin Ivory Coast, ta zargi makusantan tsohon shugaban kasar, Laurent Gbagbo, da kokarin tana zaune tsaye a kasar.

Ministan ciki gida na kasar, Sidiki Diakité, ya zayyana sunayen mutanen da suka hada da Stephane Kipre, wanda siriki ga Lauren Gbagbo da kuma Pickas Damana wadanda tun cen ma ake zargi da hannu a rikicin kasar na tsakanin shekara 2002 - 2011.

Gwanatin dai ta bayyana hakan ne bisa la'akari da  hare hare da ake kaiwa shingayen 'yan sanda da kuma na jami'an tsaron Jandarma a 'yan wattanin baya baya nan.

Bincike da aka yi dai tun bayan hare haren bakai da aka kai ya kai ga nasara kama mutane 35 ciki har da sojoji shida, a cewar wata sanarwa da ma'aikatar cikin kasar ta fitar bayan wani taro na masu ruwa da tsaki kan harkar tsaron kasar.