'Yan Adawan Angola Sun Bukaci A Soke Zabe
Wasu jam'iyun adawa uku a Angola, sun bukaci kotun tsarin mulkin kasar data soke babban zaben kasar da aka gudanar a ranar 23 ga watan Agusta da ya gabata.
A cikin wasikar da suka aikewa kotun, jam'iyyun da suka da (Unita), da FNLA da kuma PNS sun ce zaben da jam'iyyar mai mulki a kasar ta lashe da gagarimin rinjaye na cike da kurakurai.
Da ya ke karin haske akan hakan Darektan yakin naman zabe na jam'iyyar adawa ta Unita, Ruben Sikato, ya ce a cikin gundumomi 15 daga cikin 18 na kasar an sabawa dokokin zabe, a don haka ne suke bukatar kotun da kada ta amunce da sakamakon zaben da hukumar zaben kasar ta bayyana.
Yana mai karawa da cewa suna bukatar a sake kirga kuri'un da aka kada runfuna zuwa runfuna don tabbatar da gaskiya kuri'un da aka kada.