An Kama Wani Kwamandan ISIS A Birnin Kano
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23883-an_kama_wani_kwamandan_isis_a_birnin_kano
Hukumar yansandan ciki ta Nigeria reshen Kano ta bada labarin cafke wani kwamandan kungiyar yan ta'adda ta ISIS a birnin Kano kafin sallar babba da ta gabata.
(last modified 2018-08-22T07:00:40+00:00 )
Sep 10, 2017 05:38 UTC
  • An Kama Wani Kwamandan ISIS A Birnin Kano

Hukumar yansandan ciki ta Nigeria reshen Kano ta bada labarin cafke wani kwamandan kungiyar yan ta'adda ta ISIS a birnin Kano kafin sallar babba da ta gabata.

Jaridar Daily Trust ta kara da cewa hukumar DSS ta bayyana sunan mutumin da ta kama da cewa Husseini Mai Tangaran kuma yana daga cikin kwamandojin kungiyar yan ta'addan da aka dade ana nemansa.

Waji jami'in hukumar masi suna Tony Opuiyo ya fadawa Daily Trust cewa kungiyar ta IS reshen yammacin Afrika tana son kai hare-hare da bindigogi da kuma na kunar bakin wake a jihohin  Kano, Kaduna, Niger, Bauchi, Yabo, Borno da kuma Abuja a ranar Sallar da ta gabata, amma bata sami nasara ba.

Labarin ya kara da cewa Mai-tangaran yana da hannu a hare haren 20-Jenerun-2012, a ofishin AIG Zone 1 na kano da kuma na masallacin Kano da kuma wani mummunan hari kan sojoji a jihar Yobe a shekara tab 2015.