Harin Ta'addanci Ya Lashe Rayukan Mutane A Kasar Somaliya
Sep 10, 2017 13:41 UTC
Wani bom ya fashe a gidan cin abinci da ke garin Beledweyne a shiyar arewacin kasar Somaliya, inda ya lashe rayukan mutane akalla shida tare da jikkata wasu da dama.
Majiyar rundunar 'yan sandan kasar Somaliya ta sanar da cewa: Wani bom ya tarwatse a gidan cin abinci a garin Beledweyne da ke arewacin kasar Somaliya, inda fashewarsa ya janyo hasarar rayukan mutane akalla shida tare da jikkatan wasu adadi masu yawa.
Majiyar 'yan sandan ta kara da cewa: Gidan cin abincin yana kusa ne da gidan wani babban jami'in gwamnatin kasar, kuma tuni kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab ta kasar ta dauki alhakin kai harin.
Tags