AU Ta Gabatar Da Shawarwarin Warware Rikicin Libiya
Kungiyar tarayya Afrika ta AU ta gabatar da wasu shawarwari da take ganin zasu kai ga warware rikicin kasar Libiya ta hanyar siyasa.
An gabatar da shawarwarin ne bayan taron kwamitin koli na kungiyar kan rikicin kasar Libiya karo na hudu a Brazaville.
Shawarwarin dai sun hada da yin tattaunawa ta tsakanin masu rikicin na Libiya a watan Disamba mai zuwa a birnin Addis-Ababa, da kuma kaddamar da shirin mayan zabukan kasar a watan Janairun badi wanda zai farawa da zaben jin ra'ayin al'umma kan kudin tsarin mulki, sai kuma zaben 'yan majalisar dokoki kafin a kai ga zaben shugaban kasar, amman kafin duk hakan sai an kafa hukumomi da kuma gwamnatin wucin gadi.
Taron wanda shi ne irinsa na biyu bayan na watan Janairu, ya samu halatar shugawabannin kasashen Afrika ta Kudu, Jacob Zuma da kuma na Nijar, Mahammadu Issufu.