An soki Shugaban Najeria kan batun Boko Haram
An yi suka ga shugaban Najeria kan yadda yake bankama yakin da kasar ke yi da kungiyar Boko Haram.
A cikin wata hira da ya yi tare da 'yan jaridu Malam Gyari Modu daya daga cikin manyan dattijan jihar borno dake arewa maso gabashin Najeria ya zargi shugaba Muhamadu Buhari da bankama abubuwa kan batun yakin da kungiyar Boko Haram, inda ya ce maganar da ake cewa Gwamnati ta kwace dukkanin yankunan da kungiyar boko haram ta mamaye ba gaskiya ne ba.
A nasa bangare, Mahamadu Ndume daya daga cikin wakilan jihar a Majalisar Dokoki ya ce Sojojin kasar sun samu nasarar dakile duk wata hanya da 'yan kungiyar ke samun kayan abinci,da kuma ababen bukatunsu da hakan shi zai basu dama nan gaba za su kwashe dukkanin yankunan dake karkashinsu.
A makon da ya gabata ma babban kwamandan Sojojin Amurka dake kasashen Afirka ya ce har yanzu akwai wasu yankuna dake karkashin ikon kungiyar Boko Haram a jihar Borno.