Rawar Da Saudiya Ta Taka Game Da Harin 11 Ga Satumba
(last modified Wed, 13 Sep 2017 02:58:52 GMT )
Sep 13, 2017 02:58 UTC
  • Rawar Da Saudiya Ta Taka Game Da Harin 11 Ga Satumba

Wata jaridar kasar Amurka ta sake bankado sabbin hujjoji da ke nuni da cewa Saudiya tana da hannu a harin 11 ga watan satumba

A yayin da ake bukukuwan juyayin harin 11 ga watan satumba karo na 17, jaridar New York Post ta bankado wasu sabin hujjoji dake nuna rawar da saudiya ta taka a harin 11 ga watan satumba, jaridar ta ce ofishin jakadancin saudiya dake kasar Amurka ya taimaka da kudi kan yadda aka kera Bam din dake kama da jirgin sama wanda aka kai harin da shi,  an yi gwajin wannan Bam shekaru biyu kafin kai harin na 11 ga watan satumba, kuma ma'aikatan ofishin jakadancin saudiya dake kasar Amurka biyu ne suka dauki nauyin daliban da suka kera wannan Bam dake kama da jirgin sama.

Fitar da wadannan sabin hujjoji na zuwa ne a yayin da ake zargin wadanda suka kai harin ta'addancin na ranar 11 ga watan satumba 'yan asalin kasar Saudiya, rahotanni da dama sun bayyana hanun mahukunta saudiya kai tsaye a harin ta'addancin 11 ga watan  satumbar.

Cire shafi 28 na rahoton bayan da aka fitar  dake ishara game da rawar da mahukunta saudiyar suka taka wajen kai harin 11 ga watan satumbar shi ke nuna cewa magabatan Washington sun kudiri aniyar rufe duk wasu hujjoji dake bayyana irin rawar da saudiya ta taka a harin na 11 ga watan satumba, an bayyana cewa kungiyar leken asirin Amurka CIA nada hannu kai tsaye wajen lullube wannan gaskiya.

A ci gaba da makircin siyasar magabatan birnin Washington wajen gurbata tunanin al'umma, sun jinjinawa magabatan birnin Riyad game da gudumuwar da suke bayarwa wajen tabbatar da kwanciyar hankali a gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya, duk kuwa da rawan da suke takawa wajen kirkiro  'yan ta'adda tare da goyon bayansu a kasashen Siriya da Iraki, ga kuma harin wuce gona da irin  kan al'ummar kasar Yemen kimanin shekaru uku.

Ayyukan saudiya a ciki da wajen kasar na nuni da cewa mafi yawan 'yan ta'addar yankin da ma duniya  na samun taimako ne daga kasar, wannan gaskiya ba boyayya ba ce a wajen mutanan dake bin siyasar duniya, duk 'yan ta'addar dake kai hare-haren ta'addanci a duniya sun tasirantu ne daga akidar wahabiyanci, kuma suna samun taimakon kudi da makamai ne daga masarautar Ali sa'oud.a yau rawar da saudiya ke takawa a rikicni kasashen Siriya da Iraki a bayyane yake.

Masu sharhi kan al'amuran siyasar kasashen yankin gabas ta tsakiya na ganin cewa saudiya na zartar da mumunar siyasar magabatan Amurka da HKI ne don haka duk wani ta'addanci da take aiwatarwa a yankin, Duniya ke rufe ido kansa, ko harin 11 ga watan Satumban 2001  da aka kai a Amurka an sanya saudiya ne gaba domin samun damar wargaza kasashen musulmi a duniya.