Sojojin Najeriya Sun Kira Masu Fafutukar Kafa Kasar Biafra Da 'Yan Ta'adda
Rundunar sojin Najeriya ta kira madugun kungiyar IPOB da ke fafutikar kafa kasar Biafra da magoya bayansa a matsayin 'yan ta'adda.
Wata sanarwa da daraktan watsa labarai na rundunar tsaron kasar Manjo Janar John Enenche ya aikewa manema labarai, ya ce kungiyar, "ta sauya zuwa barazanar tsaro ga kasar".
Ta kara da cewa, "Bayan mun yi nazari a kan abubuwan da ke faruwa a baya bayan nan, muna son sanar da jama'a cewa ikirarin da mambobin IPOB ke yi cewa su kungiyar ba kungiyar tayar da hankali ba ce ba gaskiya ba ne. Don haka abubuwan da suke yi ta'addanci ne".
Ayyana wannan kungiya a matsayi ta 'yan ta'adda na nufin za a iya mu'amala da su kamar yadda ake yi da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda na Duniya
Sai dai matsalar da hakan ka iya janyowa ita ce ta yadda rundunar sojin ta gaza gane irin goyon bayan da kungiyar ta IPOB ke da shi a kudu maso gabashin kasar. Haka kuma ayyana su a matsayin 'yan ta'adda ka iya haifar da wata matsalar.