MDD Ta Janye Ma'aikatanta 30 Daga Sudan Ta Kudu
Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu, ta sanar da janye ma'aikatan agajinta 30 daga yankin Aburoc dake jihar Nil saboda barkewar wani rikici.
Jagoran tawagar ta UNMISS, David Shearer, ya fada cewa saboda rikicin da sake kunno kai a ranar Laraba sun janye jami'an daga yankin.
Jami'in ya ce basu da tabas akan halin da ake ciki a yankin, aman akwai fararen hula masu yawan gaske dake cikin tsaka mai wuya a yankin na Aburoc.
Mista Shearer, ya ce da akwai fararen hula kimanin dubu guda galibi mata da yara da tsofafi dake cikin yankin wanda kuma suke bukatar kula ta gaggawa.
A watan Mayu da ya gabata ne aka jibge jami'an na MDD domin taimakawa fararen hula dake ciki halin kaka-ni- kayi a fadan da ake gobzawa tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye na Sudan ta kudu.