Sudan Ta Bukaci Amurka Ta Dage Takunkumin Da Ta Kakaba Mata
(last modified Tue, 19 Sep 2017 09:13:30 GMT )
Sep 19, 2017 09:13 UTC
  • Sudan Ta Bukaci Amurka Ta Dage Takunkumin Da Ta Kakaba Mata

Shugaban kasar sudan ya bukaci mahukuntan Amurka da su dage takunkumin da suka kakabawa kasar sa.

Kafar watsa labaran Sudan ta nakalto shugaban kasar Umar Al-bachir a yayin da yake ganawa da wani gungu na kwararru da 'yan jaridun kasar Amurka na cewa ganin cewa kasar sa ta mutunta dukkanin dokokin da Amurka ta gindaya mata, kamata yayi mahukunta na Watsinton su dage takunkumin da suka kakabawa kasarsa.

Gwamnatin Shugaba Obama ta gindayawa gwamnatin sudan wasu sharuda guda biyar, wanda da zarar ta ciki su, kasar Amurka za ta dage takunkumin da ta kakabawa kasar, to sai dai ma'aikatar harakokin kasashen wajen Amurka ta bayyana cewa maganar dage takunkumin na komawa ne kan ayyukan gwamnatin sudan game da mutunta hakin bil-adama ne, domin haka a halin da ake ciki, gwamnati ba za ta iya dage wannan takunkumi ba.

A watan janairun da ya gabata ne tsohon shugaban kasar Amurka Barak Obama ya bayar da umarnin dage takunkumin tattalin arziki da kasar ta kakabawa Sudan din, da nufin bata karfin gwiwa wajen ci gaba da kokarinta na mutunta hakkokin bil-adama da kuma yaki da ta'addanci a kasar.

Mahukuntan birnin Khartoum dai na fatan Amurka ta dage takunkmin da ta kakabawa kasar tun a watan Oktoban 1997.