Sudan Tana Son Amurka Ta Cire Mata Takunkumi
(last modified Tue, 19 Sep 2017 12:24:07 GMT )
Sep 19, 2017 12:24 UTC
  • Sudan Tana Son Amurka Ta Cire Mata Takunkumi

Shugaban Kasar Sudan Umar Hassan al-Bashir ne ya bayyana bukatar ganin Amurkan ta daukewa kasarsa takunkumi a yayin ganawa da kafafen wats labarun Amurka.

Shugaban na Kasar Sudan ya ce; Bisa la'akari da cewa Amurkan ta yadda Sudan ta yi aiki da dukkanin nauyin da ya rataya a wuyanta, wajibi ne a bangarenta ta cire wa Sudan din takunkumi.

Gwamnatin Barrack Obama ta daukewa Sudan din takunkuman da aka sa mata a baya bayan da Sudan din ta yi aiki da sharudda biyar da Amurkan t agindaya mata. Sai dai gwamnatin Donald Trump ta sake mayar da takunkumin bisa dalilin cewa an ci gaba da samun tabarbarewar harkokin hakkin bil'adama.

Sudan din tana fatan ganin an cire mata takunkumin daga nan zuwa watan Augusta na wannan shekarar da ake ciki.