Kotun Kolin Kenya Ta Soki Hukumar Zaben Kasar Saboda Batun Sakamakon Zabe
(last modified Thu, 21 Sep 2017 05:44:48 GMT )
Sep 21, 2017 05:44 UTC
  • Kotun Kolin Kenya Ta Soki Hukumar Zaben Kasar Saboda Batun Sakamakon Zabe

Kotun kolin kasar Kenya ta soki hukumar zaben kasar saboda gazawar da ta nuna wajen tantance sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan da ya kama kafin ta fitar da shi.

Kotun ta bayyana hakan ne a yayin da take fitar da cikakken bayani dangane da dalilan da ya sa ta soke zaben shugaban kasar Kenyan da aka gudanar a ranar 8 ga watan Augusta inda ta ce an tabka abubuwan da suka saba wa doka.

Kotun ta ce lalle hukumar zaben ta gaza wajen tantance ingancin sakamakon zaben, duk kuwa da cewa ba ta yi ishara da su waye suke da hannu cikin wannan matsalar da aka fuskanta ba.

A ranar 1 ga watan Satumba ne dai kotun kolin ta kasar Kenya ta sanar da soke sakamakon zaben da hukumar zaben ta ce shugaba mai ci Uhuru Kenyatta ne ya lashe zaben, inda ta ce wajibi ne a sake gudanar da zaben cikin kwanaki 60.