Shugaban Afirka Ta Tsakiya Ya Soki Gwamnatin Kasar Faransa
Shugaban kasar Afirka ta tsakiya ya soki gwamnatin kasar faransa sanadiyar janye sojojin ta da ta yi daga cikin kasarsa.
Tashar Telbijin France 24 ta nakalto Faustin-Archange Touadera shugaban kasar Afirka ta tsakiya yayin da yake jawabi a zauren MDD jiya laraba ya ce matakin da gwamnatin kasar Faransa ta dauka na janye sojojin ta daga kasar Afirka ta tsakiya kuskure ne.
Har ila yau Faustin-Archange Touadera ya nuna damuwarsa kan tsanantar tashin hankali a cikin kasar sa sannan ya bukaci tura karin dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya domin tabbatar da tsaro a cikin kasar .
Tun a shekarar 2013 ne kasar Afirka ta tsakiya ta fada cikin rikicin kabilanci da addini, lamarin da yayi sanadiyar faduwar gwamnatin kasar, mutuwar mutane da dama tare da yin hijra da duban al'ummar kasar zuwa ketare.