Shugaban Kasar Kenya Ya Zargi Kotu Da Yin Juyin Mulki
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyata ya soki matakin kotun Kolin kasar da yin juyn mulki, inda ya ce hukuncin da ya haramta nasarar zabensa a matsayin sabon shugaban kasa ya yi sabani da ra'ayin al'ummar kasar kenya.
Kenyata ya yi wadannan kalamai ne a yayin da ya ke tsokaci a gidan talabijin na kasar, bayan da kotu ta sanar da matsayanta kan hujjojin soke zaben. Shugaban ya ce 'yann adawa sun yi amfani da kotun wajen yin juyin mulki.
Hukuncin kotun na ranar 1 ga watan Satumba shekara ta 2017, shi ke zama hukuncin kotu na farko da ya yi tasiri wajen rusa zaben shugaban kasa a nahiyar Afirka.
A bangare guda,hukumar zaben kasar Kenya, ta sanar da dage ranar da za'a sake gudanar da zaben shugaban kasar daga ranar 17 ga watan Oktoba zuwa ranar 26 ga watan Oktoba.
A wata sanarwa da hukumar zaben ta fitar, ta ce an dage ranar sake shirya zaben ne biyo bayan bayanai mai dauke da sarkakiya da kotun kolin kasar ta bayyana kan yadda za'a sake shirya zaben.
Dama dai Kotun kolin kasar ta Kenya, ta bada wa'adin kwanaki 60 don shirya wani sabon zabe, wato ranar 17 ga watan Oktoba. Kotun dai ta soke babban zaben da ya ya gudana a watan Agusta bayan da ta zargi hukumar zaben na rashin gabatar da sakamako mai inganci.