Sudan : Al Bashir Ya Bukaci Mazauna Darfur Su Mika Makamansu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24267-sudan_al_bashir_ya_bukaci_mazauna_darfur_su_mika_makamansu
Shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir, ya bukaci mazauna yankin Darfur da su mika makamansu ga gwamnati cikin ruwan sanyi, kafin gwamnati ta fara karba da karfi.
(last modified 2018-08-22T07:00:44+00:00 )
Sep 22, 2017 13:39 UTC
  • Sudan : Al Bashir Ya Bukaci Mazauna Darfur Su Mika Makamansu

Shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir, ya bukaci mazauna yankin Darfur da su mika makamansu ga gwamnati cikin ruwan sanyi, kafin gwamnati ta fara karba da karfi.

Da yake jawabi ga wani taron jama'a a birnin Nyala, babban birnin jihar Darfur ta Kudu, shugaba Al-Bashir ya ce, da gaske suke game da batun kwace makamai, kuma abu mafi dacewa ga duk wani da ya mallaki bindiga shi ne ya mika ta ga hukuma.

Ya kara da cewa, dole ne duk wani da ya boye makami ya mika shi ga gwamnati bisa radin kansa.

Dama kafin hakan Shugaba al Bashir ya bukaci mazauna yankin na Darfur da suka tsere daga gidajensu, da su koma gida sakamakon kawo karshen yakin da aka gwabza wanda hallaka dubban mutane.

A kalla mutane sama da miliyan biyu da rabi ne suka tsere daga yankin na Darfur, kana wasu kusan 300,000 suka rasa rayukansu a cewar MDD sakamakon tashin hankalin da ya barke cikin shekara ta 2003, tsakanin ‘yan tawaye daga kananan kabilun yankin da sojojin kasar.