Yan Kasar Morocco Kimanin 1600 Ne Suka Shiga Kungiyar Daesh
Sep 25, 2017 11:49 UTC
Majiyar gwamnatin kasar Morocco ta bada sanarwan cewa yan kasar kimani 1600 ne suka shiga kungiyar Daesh
Shafin yanar gizo na alwasad ya nakalto AbdulHaaq Alkhayyam shugaban hukumar bincike karakshin ma'aikatar sharia na kasar yana fadar haka a yau Litini, ya kuma kara da cewa wadannan yan ta'adda 1664 sun shiga kungiyar ta Daesh a ne a kasashen Libya, Iraqi da kuma Siria.
Alkhayyam ya kara da cewa a cikin kungiyoyin yan ta'adda 47 da suka gano, 42 daga cikinsu suna da dangantaka kai tsaye da kungiyar ta Daesh, sannan sun kama mutane 701 daga cikin yayansu. Khayyam daga karshe yace yan ta'adda 85 da suka je kasar Syria sun dawo kasar ta Morocco.
Tags