Chadi Ta Ji Mamakin Haramtawa 'Yan Kasarta Zuwa Amurka
Gwamnatin Chadi ta ce ta ji mamaki matuka da kuma rashin sanin dalilin sanya ta a cikin jerin kasashen da matakin shugaba Donald Trump na hana baki shiga Amurka ya shafa.
Wata sanarwa da hukumonin N'Djamena suka fitar a jiya Litini ta ce wannan abun takaici ne mai cike da mamaki sanya ta da Amurka ta yi a cikin jerin kasashen da wannan doka ta shafa.
Kakakin gwamnatin Chadi Madeleine Alingue ta ce kwata kwata wannan matakin ya yi hannun riga da kokarin da kasar ke yi wajen yaki da ta'addanci.
Ita dai Amurka ta ce ta sanya Chadi a cikin jerin kasasshen da akawa al'ummarsu haramcin sanya kafa a Amurkar saboda rashin yin hadin gwiwa da Amurka da kuma kin bada cikaken bayani akan masu balaguro zuwa Amurkar.
A jiya ne dai shugaban Amurka Donald Trump ya sanya kasar ta Chadi cikin kasashe 8 da aka harantawa ‘Yan kasarsu shiga Amurka saboda abinda ya kira matsalar tsaro da kuma rashin ba Amurka hadin kan da ya dace.
Sauran sabbin kasashen da aka bayyana sunayensu sun hada da Koriya ta Arewa da Venezuela, bayan da aka cire kasar Sudan daga cikin jerin kasashen da dokar ta shafa tun tashin farko.