Mutane 4 Sun Mutu Sakamakon Fashewar Wata Nakiya A Burkina Faso
Rahotanni daga kasar Burkina Faso sun bayyana cewar alal akalla mutane mutane hudu sun rasa rayukansu kana wasu kuma sun sami raunuka sakamakon fashewar wata nakiya a arewacin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Xianhua na kasar China ya jiyo ma'aikatar tsaron kasar Burkina Fason tana fadin cewa sakamakon fashewar wata nakiya da aka dana a kan hanyar wata babbar motar daukar makamashi a arewacin kasar, mutane hudu sun rasa rayukansu kana wasu biyu kuma sun sami raunuka.
Ma'aikatar tsaron ta kara da cewa biyu daga cikin wadanda suka mutun jami'an 'yan sanda ne sannan ita motar kuma ta tarwatse gaba daya.
Har ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhaki kai harin, to sai dai kuma masana harkokin tsaro suna dora alhakin irin wadannan hare-hare kan 'yan kungiyar Ansar al-Islam karkashin jagorancin Malam Ibrahim Dicko da ake zargi da ayyukan ta'addanci.