Takunkumin Amurka Ya Gurgunta Sudan_Al-Bashir
(last modified Thu, 28 Sep 2017 15:38:23 GMT )
Sep 28, 2017 15:38 UTC
  • Takunkumin Amurka Ya Gurgunta Sudan_Al-Bashir

Shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashin ya kalubalanci takunkumin tsawan shekaru da Amurka ta kakabawa kasarsa.

Al-Bashir ya ce takunkumin kasuwancin da Amurka ta kakabawa kasar tun shekara 1997 sun haifar da koma baya wa kasar a fannin gwamnati da kuma hukumomi tare da hadassa wahalhalu ga al'ummar kasar ta Sudan.

Nan da makwanni biyu masu zuwa ne, Shugaba Donald Trump na Amurka zai dauki mataki akan amunce dagewa kasar ta Sudan Takunkumin ko kuma A'a.

Yau shekaru 20 kenan da gwamnatin Amurka ta kakabawa gwamnatin Khartum takunkumi saboda zargin goyan bayan mayakan dake ikirari da sunan Islama.

A ranar Lahadi data gabata, Trump ya janye Sudan daga cikin jerin kasashen da dokarsa ta haramtawa sanya kafa Amurka.