UNICEF: Fiye Da Rabin Makarantu A Yankin Boko Haram Sune Rufe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24459-unicef_fiye_da_rabin_makarantu_a_yankin_boko_haram_sune_rufe
Hukumar UNICEF mai kula da yara ta MDD ta bada rahoto kan cewa mafi yawan makarantun boko a yankunan da yayan kungiyar boko haram suka fi yawan kai-kawo a cikinsu a rufe suke
(last modified 2018-08-22T07:00:45+00:00 )
Sep 29, 2017 01:37 UTC
  • UNICEF: Fiye Da Rabin Makarantu A Yankin Boko Haram Sune Rufe

Hukumar UNICEF mai kula da yara ta MDD ta bada rahoto kan cewa mafi yawan makarantun boko a yankunan da yayan kungiyar boko haram suka fi yawan kai-kawo a cikinsu a rufe suke

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Austin Forsyth mataimakin darectan hukumar ta UNICEF a birnin Abuja na tarayyar Nigeria tana fadar haka a yau Jumma'a. Ta kuma kara da cewa fiye da kashi 57% na makarantu a jihar Borno inda rikicin Boko Haram ya fi kamari a rufe suke duk da cewa an shiga sabon shekarar karatu. 

Rahoton ya kara da cewa a cikin shekaru 8 da suka gabata malaman makarantu a yankin 2,295 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar rikicin boko haram sannan wasu dubu 19,000 sun kauracewa gidajensu, a yayinda aka lalata makarantu 1400. 

Hukumar ta UNICEF ta kara da cewa ta yi kokarin budewa yan gudun hijira a wadannan yankuna makarantun wucin gadi amma tallafin da ta bukata  don aiwatar da wannan shirin bai samu ba sai  kashi 1/5 na abinda ta bukata.