Yan Bindiga Sun Sake Wani Babban Jami'in Yansanda Da Iyalansa A Zamfara
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24461-yan_bindiga_sun_sake_wani_babban_jami'in_yansanda_da_iyalansa_a_zamfara
Wasu yan bindiga wadanda ba'a tantance ko su waye ne ba sun sace wani Jami'in yansanda da iyalanda a wani wuri tsakanin Katsina da Kaduna a jiya Alhamis.
(last modified 2018-08-22T07:00:45+00:00 )
Sep 29, 2017 01:37 UTC
  • Yan Bindiga Sun Sake Wani Babban Jami'in Yansanda Da Iyalansa A Zamfara

Wasu yan bindiga wadanda ba'a tantance ko su waye ne ba sun sace wani Jami'in yansanda da iyalanda a wani wuri tsakanin Katsina da Kaduna a jiya Alhamis.

Dansandan mai suna Emmanuel Agene mai mukamin Mataikamin kwamishinan yansanda kuma wanda yake aiki da sashen bincike manya manyan laifuffuka wato CID a Gussau ya fada hannun yan bindigan ne a tsakanin Birnin -Gwari da Funtuwa inda suka tilasta masa tsayawa da motarsa, sannan suka tafi da shi tare da iyalansa ukku zuwa wani wuri.

Jami'in watsa labarai na yansanda a Jihar Zamfara DSP Mohammad Shehu ya ki ya yi magana a kan batun don sacewar ta auku ne a wajen jihar Zamfara. 

Har'ila yau wasu yan bindigan sun sace wasu yansandan ukku na daban a rana guda a tsakanin Birnin Gwari da Kaduna. Jaridar Daily Trust ta tuntubi ASP Mukhtar Husain Ali jami'in watsa labarai na yansanda a jihar Kaduna amma bai sami zantawa da shi ba.