Najeriya / Boko Haram : Kashi 57% Na Makarantu Basu Bude Ba_ Unicef
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24489-najeriya_boko_haram_kashi_57_na_makarantu_basu_bude_ba_unicef
Asusun kula da yara kanana na MDD wato Unicef ya fitar da wani rahoto dake cewa rabin makarantun boko a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya dake fama da matsalar boko Haram basu sake bude kofofinsu ba.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Sep 30, 2017 02:09 UTC
  • Najeriya / Boko Haram : Kashi 57% Na Makarantu Basu Bude Ba_ Unicef

Asusun kula da yara kanana na MDD wato Unicef ya fitar da wani rahoto dake cewa rabin makarantun boko a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya dake fama da matsalar boko Haram basu sake bude kofofinsu ba.

A rahoton da ya fitar Jiya Juma'a, Asusun na Unicef ya ce hakan na nufin sama da kashi 57% na makarantun yankin musamen a Borno na ci gaba da kasancewa a rufe har yanzu saboda matsalar ta Boko haram. 

Asusun na Unicef ya ce makarantun basu samu damar budewa ba saboda barna da aka aikata ba tada misali, kuma mafi yawansu suna a wurare dake da hadarin gaske.

Rahoton ya ce tun daga shekara 2009, sama da maluman makarantu da 2,295 ne aka kashe, kana kusan makarantu 1,400 ne aka lalata.

Alkaluman da MDD ta fitar sun nuna cewa yara milyan daya ne suka bar gidajensu saboda yakin da ake gwabzawa tsakanin mayakan Boko haram da sojojin Najeriya.