Najeriya : Za'a Wa Wasu ‘Yan Boko Haram Shari'a A Asirce
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24493-najeriya_za'a_wa_wasu_yan_boko_haram_shari'a_a_asirce
Bayanai daga Najeriya na cewa za' a yi shari’ar wasu da ake zargi ‘yan kungiyar Boko Haram ne a asirce.
(last modified 2018-08-22T07:00:46+00:00 )
Sep 30, 2017 02:51 UTC
  • Najeriya : Za'a Wa Wasu ‘Yan Boko Haram Shari'a A Asirce

Bayanai daga Najeriya na cewa za' a yi shari’ar wasu da ake zargi ‘yan kungiyar Boko Haram ne a asirce.

Rahotanni sun ce ba dai za'a baiwa ‘yan jarida damar halartar zaman kotun ba.

wata majiyar sharia a Najeriya ta ce shaidawa kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa ‘yan kungiyar Boko Haram 1,600 ne za'a wa shari'ar.

Majiyar ta kara da cewa an tsayar da wannan shawara ne saboda matakan tsaro bayan tattaunawa tsakanin Jami’an gwamnati da kuma jami’an tsaro na farin kaya.

A ranar 9 ga watan gobe ne ake sa ran fara shari'ar masu zargin da ake tsare dasu a wuraren daban-daban.

Kafin hakan dai wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam sun dade suna sukar jami’an tsaron Najeriya da kame fararen hula da sunan ‘yan Boko Haram ba tare da an gurfanar da su a kotu ba.