Gwamnatin Sudan Ta Kudu Zata Rufe Wasu Ofisoshin Jakadancinta Sakamakon Matsalar Kudi
Gwamnatin Sudan ta Kudu ta sanar da cewar zata rufe wasu daga cikin ofisoshin jakadancinta da suke wasu kasashen duniya zuwa wani lokaci sakamakon matsalar kudi.
Shafin Al-Nile na kasar Masar a yau Talata ya watsa labarin cewa; Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta Kudu ta sanar da cewa; Gwamnatin kasar zata rufe wasu daga cikin ofisoshin jakadancinta da suke kasashen nahiyar Turai, Amurka, Afrika da Asiya da yawansu ya kai 24 na wani dan gajeren lokaci saboda matsalar karancin kudade da kasar ke fuskanta musamman a fagen kasafin kudi da gwamnatin ke son gabatarwa.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sudan ta Kudu ta kara da cewa; Gwamnatin Sudan ta Kudu tana fama da matsalar karanci kudade da ba zata iya biyan kudaden hayar ofisoshin jakadancinta da suke kasashen duniya ba gami da na kananan ofisoshin jakadancinta da kuma biyan kudaden albashin ma'aikatan nata da suke wajen kasar.