Shugaba Buhari: Ba Zan Yarda Da Shirin Raba Nijeriya Ba
Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya yayi karin haske dangane da irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fagagen tattalin arziki da tsaro yana mai cewa ba zai taba amincewa da kiran da wasu suke yi na raba Nijeriya da kuma ballewa ba.
Shugaba Buharin ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi wa 'yan Nijeriyan a safiyar yau a daidai lokacin da kasar take cika shekaru 57 da samun 'yancin kai inda ya ce yayi yaki na tsawon shekaru lokacin yakin basasa don tabbatar da hadin kan Nijeriya don haka ba zai taba bari wasu wadanda ba a haife su ba ma lokacin da aka yi yakin basasar su rarraba Nijeriya.
Shugaba Buharin dai yana ishara ne da tsagerun inyamurai 'yan kungiyar nan ta IPOB da suke son kafa kasar Biafra inda ya nuna bakin cikinsa da yadda dattawan yanki suka zuba ido wadannan yara suna abin da suka so ba tare sun ja kunnensu ba, yana mai sake jaddada abin da ya sha fadi cewa duk wanda yake da wani korafi to ya kai gaban majalisar dokoki ta kasa ko kuma ta jiharsa don dubi cikin lamarin.
A wani bangare na jawabin nasa shugaba Buharin yayi ishar da irin nasarorin da gwamnatin tasa ta samu a fagagen tattalin arziki da kuma tsaro, duk kuwa da matsalolin da ake fuskanta yana mai shan alwashin ci gaba da kokari wajen ganin an magance matsalolin da ake fuskanta.
Nigeria din dai ta sami 'yancin kai daga wajen turawan Ingila ne a ranar 1 ga watan Oktoban 1960 don haka a kowace shekara a kan gudanar da bukukuwan wannan rana idan ta zagayo.