Hukumar "UNICEF" Ta Yi Gargadi Kan Bullar Masifar Yunwa A Kasar Zimbabwe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2455-hukumar_unicef_ta_yi_gargadi_kan_bullar_masifar_yunwa_a_kasar_zimbabwe
Asusun kula da kananan yara da mata na Majalisar Dinkin Duniya "UNICEF" ya yi gargadi dangane da bullar masifar yunwa da karancin kayayyakin abinci masu gina jiki da kananan yara suke bukata a kasar Zimbabwe.
(last modified 2018-08-22T06:57:59+00:00 )
Mar 15, 2016 14:32 UTC
  • Hukumar

Asusun kula da kananan yara da mata na Majalisar Dinkin Duniya "UNICEF" ya yi gargadi dangane da bullar masifar yunwa da karancin kayayyakin abinci masu gina jiki da kananan yara suke bukata a kasar Zimbabwe.

Wakilin Asusun Kula da Kananan Yara da Mata na Majalisar Dinkin Duniya "UNICEF" a kasar Zimbabwe John Miyouta ya bayyana cewa; Yau tsawon shekaru 15 ke nan rabo kasar Zimbabwe da fuskantar matsalar kayayyakin abinci masu gina jiki da yara suke bukata, inda a halin yanzu haka akwai kananan yara da yawansu ya haura 33, 000 da suke bukatar kayayyakin abinci masu gina jiki a kasar.

A gefe guda kuma kakakin Asusun Kula da Kananan Yara da Mata "UNICEF" a kasar ta Zimbabwe Victor Chinayamo ya bayyana cewa; Matsalar fari a wannan shekara ta janyo karancin kayayyakin abinci a Zimbabwe lamarin da zai kara bullar matsalar karancin abinci da yunwa a tsakanin al'ummar kasar.