Majalisar Alkalai Ta NJC Ta Kafa Kwamitin Binciken Aikalai
Majalisar alkalai ta kasa a tarayyar Nijeriya ta NJC ta kafa kwamiti don binciken manya manyan alkalai 2 da kuma wasu 13 a jiya litinin kan zargin aikata ba daidai ba
Jaridar Premium Times ta Nigeria ta bada rabarin cewa majalisar alkalan ta dauki wannan matakin ne bayan karban rahotanni kimani 46 da suke zargin wasu alkalan da aikata ba daidai ba.
Majalisar karkashin jagorancin alkalin alkalan kasa Walter Onnoghen ta dauki wannan matakin ne a taronta na 83 wanda aka gudanar a jiya litinin a Abuja. Har'ila yau labarin ya kara da cewa majalisar ta yi watsi da korafe korafe 31 wanda basu da kwakwaran shaidu kan zarge zargen.
Banda haka majalisar alkalan ta yaba da wasikar gwamnan jihar Zamfara na tabbatar da tube Musa Anka a matsayin alkali a jihar bayan an tabbatar da cewa ya karbi cin hanci na Naira 200,000 daga wani mutum mai suna Zubairu Abdulmalik don ya yanke hukunci irin yadda yake so.
Majalisar ta gabatar da wannan bukatar ne ga gwamnatin Jihar Zamfara tun shekara 2011 amma bata aiwatar da shi ba sai yanzu.