Gwamnatin Somaliya Za Ta Sanya Ido Kan Kamfanonin Sadarwa
Oct 03, 2017 10:52 UTC
Gwamnatin Somaliya ta fitar da wata sabuwar doka da zata sanya ido kan kamfanonin sadarwa a kasar.
Wannan dai shi ne mataki irinsa na farko a kasar ta Somaliya cikin shekaru 30, kuma shugaban kasar Mohamed Abdullahi Farmajo, ya danganta dokar da mai cike da tarihi.
Kafin wannan doka dai kamfanonin sadarwa a wannan kasa ta Somaliya sun ne ke da wuka da nama akan gudanar da aikinsu.
koda yake gwamnatin bata yi karin haske ba kan dokar, aman kwararu sun ce dokar zata sanya ido kan layukan kira da ake sayarwa jama'a saboda dalilai na tsaro.
Kasar Somaliya dai ta jima tana fuskantar barazana 'yan ta'adda na Al'Shabab dake kai hare hare nan da cen a cikin kasar.
Tags