Sojojin Somaliya Sun Kai Farmaki Kan Maboyar 'Yan Ta'addan Kungiyar Al-Shabab
Oct 03, 2017 18:58 UTC
Sojojin gwamnatin Somaliya sun kai farmaki kan maboyar 'yan kungiyar Al-Shabab da ke shiyar kudancin kasar, inda suka yi nasarar halaka 'yan ta'adda tara.
Majiyar rundunar sojin Somaliya a yau Talata ta sanar da cewa: Sojojin kasar sun kai farmaki kan maboyar 'yan kungiyar Al-Shabab da ke yankin Gedo a shiyar kudancin kasar, inda suka yi nasarar kashe 'yan ta'adda tara tare da kwasar ganimar makamai masu yawa.
Hari kan maboyar 'yan ta'addan na kungiyar Al-Shabab a yankin Gedo ya zo ne kwana guda da 'yan ta'addan na Al-shabab suka kaddamar da wasu jerin hare-haren wuce gona da iri kan garuruwan kasar Somaliya da suke kusa da kan iyaka da kasar Kenya.
Tags