Nijeriya : An Gano Gawarwaki 16 Bayan Kifewar Kwale-kwale A Kebbi
Oct 05, 2017 06:55 UTC
A Nijeriya ana ci gaba da neman wasu gawawakin mutanen da hatsarin kwale kwale ya rusa da su a jihar Kebbi dake arewacin kasar.
Kawo yanzu dai an tsinto gawawarki 16 daga cikin mutum sama da 60 da kwale-kwale ya nitse da su a ranar talatan da ta gabata a garin Yawuri na jihar ta Kebbi.
Ana dai fargabar adadin wadanda suka mutu sanadin kifewar kwale kwalen ya karu, a yayin da akayi nasara ceto wasu uku da rai.
Bayanai sun nuna cewa kwale-kwalen ya bamki wani icce ne lamarin da ya sanya ya kife a tsakiyar kogin kwara.
Alkalumman da masu aikin ceto suka fitar sun nuna cewa sama da mutum 100 ne suka gamu da ajalinsu a irin wannan hatsarin a cikin wattani uku da suka gabata.
Tags