Dakarun Hadin Gwiwan Kasashen Sahel Sun Fara Gudanar Da Ayyukansu
Jaridar Le Monde ta kasar Faransa ta sanar da cewa nan ba da jimawa ba dakarun hadin gwiwa na kasashen kungiyar G5 na yankin Sahel za su fara gudanar da ayyukansu na hadin gwiwa da nufin fada da kungiyoyin 'yan ta'adda da suke yankin.
Jaridar ta bayyana cewar a jiya ne ministar tsaron kasar Faransa Florence Parly, a yayin wata ziyara da ta kai helkwatar dakarun kungiyar G5 din da ke birnin Yamai na kasar Nijar ta bayyana cewar a karshen watan Oktoban nan da muke ciki ne ake sa ran dakarun hadin gwiwan za su fara gudanar da aikinsu na kai hare-hare na dadin gwiwa.
Shi ma a nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar Faransan Jean-Yves Le Drian ya ce an kafa wannan hadin gwiwan ne da nufin fada da kungiyoyin 'yan ta'adda da suke yankin da kuma sake tsara yanayin tsaron yanki.
Hadin gwiwan dakarun kungiyar ta G5 dai ta kumshe kasashen Chadi, Nijar, Burkina Faso, Mali da kuma Mauritaniyya.