Sudan Ta Katse Hulda Da Koriya Ta Arewa
Kasar Sudan ta katse duk wata hulda da Koriya ta Arewa, a wani abu da ake ma kallon cika sharudan da AMurka ta guidaya mata ne kafin a dage mata katunkumi.
Wani jami'in gwamnatin Sudan din ya shaida a yanzu kasarsa ta cika duk sharudun tare da fatan za'a dage mata takunkuman.
A ranar 12 ga watan Oktoban nan ne gwamnatin Washington za ta yi bayyani game da batun cirewa Sudan din takunkumin tsawan shekaru 20 da aka kakaba mata na karya tattalin arziki saboda zargin goyan bayan mayakan dake ikirari da sunan Islama.
A watan Yuli da ya gabata shugaba Trump ya tsawaita matakinsa na dagewa Sudan takunkuman da wata uku.
A watan Satumban da ya gabata Shugaba Omar El Bachir na Sudan ya kalubalanci takunkumin na Amurka wanda ya ce ya gurgunta kasarsa sosai.