Somaliya: sojoji Sun Sanar Da Kashe 'Yan Kungiyar al-Shabab
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24687-somaliya_sojoji_sun_sanar_da_kashe_'yan_kungiyar_al_shabab
A yau Juma'a ne dai sojojin kasar ta Somaliya suka sanar da kashe 'yan kungiyar ta al-shabab mai alaka da al'ka'ida su 3.
(last modified 2018-08-22T07:00:47+00:00 )
Oct 06, 2017 14:38 UTC
  • Somaliya: sojoji Sun Sanar Da Kashe 'Yan Kungiyar al-Shabab

A yau Juma'a ne dai sojojin kasar ta Somaliya suka sanar da kashe 'yan kungiyar ta al-shabab mai alaka da al'ka'ida su 3.

Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya nalato cewa, baya ga yan ta'addar 3 da aka kashe, an kuma jikkata wasu 4. "Yan ta'addar dai sun kai farmaki ne akan wani sansanin soja da ke garin Baredeh da ke kudu da birnin Magadishu.

Mazauna garin na Barireh sun yi hijira saboda yadda ake batakashi mai tsanani a tsakanin 'yan ta'addar da kuma soja.

A makon da ya gabata ma dai sojojin kasar Sun kashe yan kungiyar ta al-shabab 18 da suka kai hari akan wannan sansanin da ke garin Baredeh