Madagascar: Cutar Kwalara Ta Kashe Mutane Fiye Da 30
Oct 06, 2017 18:52 UTC
Jami'an Gwamnatin kasar ta Madagascar ne suka sanar da yaduwar cutar kwalara a cikin kasar, tare da daukar rayukan mutane 33.
Tashar telbijin din France 24 ta ambato jami'an gwamnatin kasar ta Madagascar suna cewa; cutar ta barke ne tun farkon watan Augusta.
Tuni aka rufe jami'oin da suke babban birnin kasar, Antananarivo saboda hana yaduwar cutar a tsakanin dalibai.
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta yi gargadin barkewar cutar da yaudwar ta a cikin kasashen Afirka da dama.
Tags