Madagascar: Cutar Kwalara Ta Kashe Mutane Fiye Da 30
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24693-madagascar_cutar_kwalara_ta_kashe_mutane_fiye_da_30
Jami'an Gwamnatin kasar ta Madagascar ne suka sanar da yaduwar cutar kwalara a cikin kasar, tare da daukar rayukan mutane 33.
(last modified 2018-08-22T07:00:48+00:00 )
Oct 06, 2017 15:22 UTC
  • Madagascar:  Cutar Kwalara Ta Kashe Mutane  Fiye Da 30

Jami'an Gwamnatin kasar ta Madagascar ne suka sanar da yaduwar cutar kwalara a cikin kasar, tare da daukar rayukan mutane 33.

Tashar telbijin din France 24 ta ambato jami'an gwamnatin kasar ta Madagascar suna cewa; cutar ta barke ne tun farkon watan Augusta.

Tuni aka rufe jami'oin da suke babban birnin kasar,  Antananarivo saboda hana yaduwar cutar a tsakanin dalibai.

Hukumar lafiya ta duniya (WHO)  ta yi gargadin barkewar cutar da yaudwar ta a cikin kasashen Afirka da dama.