Mutane 33 Ne Suka Rasa Rayukansu Sanadiyyar Annobar Cutar Sankarau A Madagaska
Gwamnatin kasar Madagaska ta bayyana cewa ya zuwa yanzu mutane 33 ne suka mutu daga cikin watan Augustan wannan shekara sanadiyyar annoban cutar sankarau a kasar
Tashar talabijin ta France24 ta kasar Faransa ta nakalto jami'an gwamnatin kasar suna fadar haka a jiya Jumma'a, sun kuma kara da cewa mutane 200 suka kamu da cutar tun lokacin.
Baya ga haka labarin ya kara da cewa a matakan hana yaduwar wannan cutar gwamnatin kasar ta bada umurnin rufe jami'ar Antananarivo don feshin maganin hana yaduwar cutar, sannan ta samar da wurare na kiwon lafiya masu yawa a wurare daban-daban a duk fadin kasar.
Annobar Cutar Sankarau dai tana daga cikin cututtuka masu yaduwa tsakanin mutane kuma tana kama mutane da dabbobi.