Taron Wakilan Kasashen Afrika Da Faransa Don Bunkasa Dangantakar Bangarorin Biyu
(last modified Sat, 07 Oct 2017 06:44:55 GMT )
Oct 07, 2017 06:44 UTC
  • Taron Wakilan Kasashen Afrika Da Faransa Don Bunkasa Dangantakar Bangarorin Biyu

An kammala taron kwanaki biyu na kasashen Afrika da Faransa don bunkasa dangantaka tsakanin bangarorin biyu a fagen tattalin arziki, siyasa da kuma zamantakewa.

Tashar radio da kasa da kasa ta kasar Faransa ta bayyana cewa an gudanar da wannan taron wanda ya sami halartar kasashe 30 a birnin Nairobi na kasar Kenya, taron  ya tabo batutuwa daban daban na kyautata harkokin kasuwanci zamantakewa siyasa da kuma kiwon lafiya a tsakanin bangarorin biyu. 

A daidai lokacin da ake gudanar da wannan taron a kasar Kenya yan adawa sun gudanar da zanga-zangar kan yadda ake son gudanar da zaben shugaban kasa a kasar karo na biyu.

Gwamnatin kasar Farsansa ce ta jagoranci wannan taron, da nufin ganin ta bunkasa dangantakar kasuwanci da wadannan kasashe, duk kuwa da cewa gwamnatin kasar Faransa ta dade tana jujjuya lamura a kasashe da dama a nahiyar Afrika.