Sudan Ta Yi Maraba Da Matakin Dage Mata Takunkumi
Oct 07, 2017 11:01 UTC
Gwamnatin Sudan ta yi maraba da matakin da Amurka ta dauka na dage ma ta takunkuman karayar tattalin arziki da ta kakaba ma ta na tsawon shekaru 20.
Sudan ta kuma bukaci Amurka da ta janye kasar daga jerin sunayen kasashen da ta ce, suna tallafa wa ayyukan ta’addanci.
Amurka dai ta ce ta dauki matakin ne saboda ci gaban da Sudan ta samu wajen mutunta hakkin dan Adam.
Saidai tuni wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama suka nuna damuwa akan matakin na Amurka.
Ko baya ga hakan kuma kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC na neman shugaban kasar ta Sudan, Omar Hassan al Bashir ruwa a jallo kan zargin cin zarafin adama.
Tags