Najeriya : Mutane 22 Suka Mutu A Harin Masalacin Maiduguri
Mar 16, 2016 07:43 UTC
Rahotanni daga Najeriya na cewa mutane 22 ne suka rasa rayukan su sakamakon wani hari da ake kautata zaton na kunar bakin wake a wani masalaci dake Maiduguri a arewa maso gabashin kasar.
Harin na Asubahin yau Laraba wanda ake dangatawa dana kungiyar Boko Haram ne ya kuma yi sanadin jikkatar mutane da dama a cewar wasu majiyoyin asibiti.
Wasu rahotanni sun ce 'yan kunar bakin waken sun shiga masallacin ne na yankin Umurari Molai da ke Maidugurin, yayin da mutane ke cikin sallah suka dasa bama-baman.
Tags