Wata Kotu Yankewa Mayakan Boko Haram 45 Hukuncin Dauri
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24891-wata_kotu_yankewa_mayakan_boko_haram_45_hukuncin_dauri
Wata babban kotun tarayyara a Nigeria ta yanke hukuncin dauri kan wasu mayakan kungiyar Boko Haram 45 wadanda ta tabbatar da laifi a kansu
(last modified 2018-08-22T07:00:49+00:00 )
Oct 13, 2017 15:33 UTC
  • Wata Kotu Yankewa Mayakan Boko Haram 45 Hukuncin Dauri

Wata babban kotun tarayyara a Nigeria ta yanke hukuncin dauri kan wasu mayakan kungiyar Boko Haram 45 wadanda ta tabbatar da laifi a kansu

Jaridar daily Trust ta Nigeria ta nakalto ministan watsa labarai Alhaji Lai mohammad yana fadar haka a yau ta bakin mai bashi shawara na musamman Mr Segun Adeyemi.

Ministan ya ce wannan shi ne zagaye na farko na zaman kotun da aka gurfanar da wadanda ake tuhuma da hannu cikin rikicin boko haran su 575. Babban kotun ta sallami mutane 468 wadanda ya bukaci a basu horarwa ta sake shiga cikin jama'a kafin a mikasu ga gwamnatocin jihohinsu.

Sai kuma wasu mutane 34 da ta suke tuhumar da ake masa a yayinsa ta wasu 28 kuma za'a ci gaba da sauraron kararsu nan gaba a Abuja da Minna. Kotun ta dage karar sauran wadanda ake tuhuma zuwa watan Jenerun shekara ta gabata.

Ministan ya kammala da cewa za'a gurfanar da wadanda ake tuhuma 1,669 a cikin kwanaki 90. Ya ce dole ne a gurfanar da wadan nan mutane a gaban kotu a cikin lokacin da aka kayyade ko kuma a sake su ba tare da wani sharadi ba.