Shugaban Kasar Kenya Ya Sanya Hannu Kan Sabuwar Dokar Zabe Na Kasar
Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, ya sanya hannu kan sabuwar dokar zabe ta kasar da ta janyo kace-nace yana mai sanar da waye kimanin dala miliyan 100 don gudanar da zaben shugaban kasar da ake sa ran za a sake gudanar da shi a ranar 26 ga watan Oktoban nan.
A wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ta bayyana cewar a jiya Juma'a ne shugaba Kenyattan ya sanya hannu kan sabuwar dokar wacce za ta share fagen gudanar da zaben shugaban kasar wacce a baya kotun kolin kasar ta soke da kuma kiran da a sake gudanar da zaben a karshen watan Oktoban.
Sabuwar dokar dai wacce majalisar kasar ta amince da ita a ranar Larabar da ta gabata ta bayyana cewa matukar dai wani dan takara ya janye daga zaben to kai tsaye daya dan takarar ya lashe zaben kenan, kamar yadda kuma ta takaita karfin da kotun kolin kasar take da shi na soke zaben da aka gudanar da kuma wasu sharudda na zaman shugaban hukumar zaben kasar da kuma hakkin da kwamishinonin zabe suke da shi na sanar da sakamakon zaben.
Sabuwar dokar dai ta haifar da kace-nace da zanga-zangogi daga wajen gamayyar jam'iyyun adawa inda babban dan takaran jam'iyyar adawar Raila Odinga, wanda kuma ya sha kaye a zaben da aka gudanar a watan Augustan da ya gabata, ya sanar da janyewarsa daga zaben da za a gudanar nan gaba din, sai dai kuma ya ki amincewa ya sanya hannu kan takardar da ta bukaci ya sanya hannu don sanar da janyewar tasa.